Daukaka Kara: Abba ya Dauko Hayar Lauyan da ya jagoranci Kare Tinubu

 

Abba Kabir Yusuf ya samu shigar da kara a babban kotu domin kalubalantar shari’ar zaben Kano.

Gwamnan jihar Kano da jam’iyyarsa ba su gamsu da nasarar da kotu ta ba Nasiru Yusuf Gawuna ba.

Lauyan da yake kare Bola Tinubu a kotun zabe, Wole Olanipekun SAN shi ne zai tsayawa NNPP.

Kano – Abba Kabir Yusuf ya daukaka kara domin kalubalantar kotun sauraron korafin zaben gwamnan jihar Kano da ta karbe ikonsa.

Mai girma Abba Kabir Yusuf bai gamsu da hukuncin da aka yi a baya ba, Hasan Sani Tukur ya sanar da cewa gwamnan ya daukaka kara.

Gwamnan jihar Kano ya na fatan a rusa umarnin da kotu ta bada na ba Nasiru Yusuf Gawuna mulki a sakamakon zaftarewa NNPP kuri’u.

Siyasar Kano: Shari’ar Abba v Gawuna

Abba Yusuf ya shigar da kara mai lamba EPT/KN/GOV/01/2023 ta karkashin jam’iyyar NNPP a ranar 2 ga Oktoba a kotun daukaka kara.

Vanguard ta ce Gwamnan ya roki kotun ta yi sabon hukunci na dabam, ya na zargin alkalan kotun sauraron korafin zabe da sabawa dokar kasa.

Hukuncin Zoom ya saba doka – Abba

Tun farko, Abba Gida Gida kamar yadda aka fi saninsa, ya ce kotun ta sabawa tsarin mulki da ta gabatar da bakon hukunci ta manhajar Zoom.

Lauyan Gwamnan na NNPP ya ce kin zama a zauren kotu domin yin hukuncin ya ci karo da sashe na 36(3) na kundin tsarin mulkin Najeriya.

Rahoton Premium Times ya ce lauyoyin da su ka daukaka kara su na ikirarin zaftarewa NNPP kuri’u 165,616 ya ci karo da dokokin zabe.

Har ila yau, Gwamnan ya fadawa kotu cewa jam’iyyar APC ba ta gabatar da shaidu daga rumfuna da su ka yi bayani a kan kuri’un da aka soke ba.

Sannan jam’iyyar NNPP ba ta yarda Nasiru Yusuf Gawuna ya samu kuri’un da ake bukata daga biyu bisa ukun kananan hukumomin Kano ba.

An dauko Wole Olanipekun SAN

Abba ya ce an yi kuskure da aka yi hukunci da takardun zaben da ba a san daga ina su ka fito ba, lauyansa a shari’ar shi ne Wole Olanipekun SAN.

Wole Olanipekun ne ya jagoranci lauyoyin da su ka kare Bola Tinubu a shari’ar zaben shugaban kasa tsakaninsa da Atiku Abubakar da Peter Obi.

Ku na da labari sauran lauyoyin APC sun hada da: Muiz Banire, Ahmed Raji, Akin Olujimi, Yusuf Ali da Lateef Fagbemi wanda ya zama AGF.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com