Jigilar Shanun da Ake Sacewa Shi ya Kara Tura Kasar Nan Cikin Matsalar da ta ke Ciki – Sheikh Gumi
Sheikh Ahmad Gumi, ya sake jaddada cewa, ba laifin ‘yan bindiga ne yadda suke aikata barna.
Ya ce, mafi yawan shanun da ake sacewa daga yankin Arewa ana kasuwancinsu ne a kudanci.
A cewarsa, jigilar shanun da ake sacewa shi ya kara tura kasar nan cikin matsalar da ta ke ciki.
Read Also:
Kaduna – Malamin addinin Islama, Ahmad Gumi, ya bayyana cewa mafi yawan shanun da aka sace a jahar Zamfara da wasu jahohin Arewa maso yammacin kasar ana jigilar su zuwa kudancin kasar ne – kudu maso gabas, kudu maso kudu da kudu maso yamma a matsayin abinci.
Ya yi wannan fallasa mai ban al’ajabi ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a shafin sa na Facebook ranar Litinin, 6 ga Satumba.
A cewarsa, wannan satar ta taimaka wajen kara ta’azzarar matsalar ‘yan bindiga da ake fuskanta a kasar a yau ba kadan ba.
Gumi yace:
“Daga cikin halin da ake ciki, a shekarar 2009 satar shanu ya zama ruwan dare. Yawancin shanun da aka sace sun nufi kudu dasu a cikin tirela inda ake siyarwa ana yanka su.
“Wannan babban jigila na satar shanu ya rage yawan samar dasu. Mafi yawan satar da farko ya shafi makiyaya na karkara kuma ya zama mafi yawa a yankin Arewa maso yamma.”