Jirgin Ruwan da Mayaƙan Houthi Suka Kai wa Hari a Yemen ya Nutse
Hukumar tsaron ruwa ta Birtaniya ta ce ana kyautata zaton wani jirgin ruwan kasuwanci da mayaƙan Houthi suka kai wa hari a gabar tekun Yemen mako guda da ya gabata ya nutse a Maliya.
Read Also:
Jirgin ruwan mallakar ƙasar Girka mai suna MV Tutor, ya fuskanci mummunar ambaliyar ruwa bayan da wani jirgin ruwa marar matuƙi ya same shi.
Houthawan sun yi iƙirarin cewa mai jirgin yana da alaƙa da Isra’ila.
Wannan shi ne karo na biyu da wani jirgin ruwa ya nutse a hare-haren mayaƙan Houthi tun watan Nuwamba.
Tun bayan fara yaƙin Gaza ne ƙungiyar ke kai hare-hare kan jiragen ruwa a tekun Bahar Maliya, lamarin da ya haifar da cikas ga harkokin kasuwancin duniya.