Kacici-Kacici Kan Rayuwar Annabi Muhammad SAW#MAULUD
An fara wallafa wannan kacici-kacici ne a shekarar 2019 da ta gabata, wato 1441 bayan hijira kenan, sai muka sake wallafa ta a yau.
Galibin Musulmi sun yi amanna cewa ranar 12 ga watan Rabi’ul Awwal aka haifi Annabi Muhammadu SAW – akwai sabanin malamai game da wannan batu.
Saboda rinjayen wadanda suka yarda da ingancin wannan kauli ne muke gabatar maku da wannan kacici-kacici domin auna saninku game da rayuwarsa.
Sai ku shiga ciki domin gwada hazakarku.
Mun bai wa malamai sun duba amsoshin domin tabbatar da sahihancinsu.
Kacici-kacicin kan rayuwar Annabi SAW
Galibin Musulmi sun yi amanna cewa ranar 12 ga watan Rabi’ul Awwal aka haifi Annabi Muhammadu, SAW – akwai sabanin malamai game da wannan batu. Saboda rinjayen wadanda suka yarda da ingancin wannan kauli ne a yau muke gabatar muku da wannan kacici-kacici don auna iya saninku game da rayuwarsa.
Sau nawa Allah Ya kira shi Muhammad a Al-Kur’ani?