CBN ta Fitar da Tsarin shirin Buhari na Raya Matasa da Biliyan 75

 

  Babban Bankin Najeriya ta fitar da tsarin yadda za a tallafa wa matasa da jari karkashin shirin gwamnatin taraya da ta ware naira biliyan 75 domin tallafa wa matasan.

Babban Bankin ya fara fitar da kason farko naira biliyan 12.5 daga cikin kuɗin domin bunƙasa matasa.

Sannan CBN ya bayyana ƙaramin bankin NIRSAL da ke ƙarkshinsa a matsayin wanda zai tafiyar da shirin.

Gwamnati ta ce shirin ya shafi samar wa matasa 500,000 ayyukan yi waɗanda za su amfana da shirin duk shekara tsakanin 2020 zuwa 2023.

Tsarin ya shafi matasa ƴan tsakanin shekaru 18 zuwa 35 da gwamnati za ta tallafawa waɗanda ke da tunani na kasuwanci

CBN ya bayyana a shafinsa na intanet cewa tsarin tallafin zai dogara ne a tsarin kasuwancin mutum, inda zai iya samu bashin naira 250,000 na jari.

Ga abubuwa uku da suka kamata ku sani game da tallafin da kuma yadda za ku tura buƙatarku:

  • 1. Wa ya cancanta?

A bayanan da gwamnati ta fitar ta ce sai ƴan tsakanin shekara 18 zuwa 35 da suke da tunani na kasuwanci kuma suke buƙatar tallafin kuɗi ne za su iya neman wannan tallafi.

  • 2. Me ya sa gwamnati ta ƙaddamar da tallafin?

Tallafin kuɗin ya shafi zuba jari ga tunanin matasa na kasuwanci da basirar da suke da ita.

Gwamnati ta yi imanin cewa za ta sauya tunanin matasan su koma dogaro da kansu ta yadda za su taimaka wa ci gaban ƙasa. Shirin na tsawon shekara uku ne.

  • 3. Ta yaya za ka samu tallafin?

Mai taimaka wa shugaban ƙasa kan kafofin sadarwa na intanet, Lauretta Onochie, ta bayyana cewa matasan da ke son tura buƙatarsu za su shiga wannan shafin, a nan

Amma kafin cike fom ɗin tura buƙata, dole sai mutum ya tabbata yana da lambobin banki na BVN.

Gwamnati za ta saki naira biliyan 25 duk shekara har shekara uku da za a kammala shirin.

Shirin na gwamnatin Buhari domin magance matsalar rashin ayyukan yi ga matasa, shiri ne mai ɗorewa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here