Gwamnatin Kaduna ta ƙaddamar da Cibiyar Haɗin Kan Addinin Musulmi da Kirista a jahar
Gwamnan Kaduna Malam Nasir el-Rufai, ya ƙaddamar da cibiyar binciken nazarin haɗin kan addinin Musulmi da Kirista a jahar.
A cikin jawabinsa da ya wallafa a a shafinsa na Facebook a bikin kafa tubalin ginin cibiyar, gwamnan ya ce cibiyar da za ta mayar da hankali kan tabbatar da zaman lafiya a jahar Kaduna ta hanyar ilimin da ya shafi harakokin addinai
Read Also:
Ya kuma bayyana goyon baya ga koƙarin malamin addinin Kirista Bishop Fearon kan taimakonsa na ganin an kawar da abin da ya kira “jahilci ya da gurɓata alaƙa tsakanin addinai a jahar Kaduna.”
Ya kuma ce wannan zai kawar da gubar jahilci wanda ya ba wasu da dama ɗaukar addininsu a matsayin lasisin cin zarafin mabiya wasu addinai.
A watan Oktoba gwamna El-Rufai ya ƙaddamar da hukumar da za ta sa ido ga harakokin addini da ya kunshi har da masu wa’azi a jahar.
A 2019 kotu ta yanke hukuncin cewa gwamnati tana da ƴancin daidaita ayyukan addini a jahar bayan wani ɓangare na addini ya ƙalubalanci gwamnatin El-Rufai.