An Kama Mutane 12 da Ake Zargi da Kashe Matafiya Musulmai 25
Rundunar sojojin Najeriya a jahar Filato sun cafke wasu mutune 12 da ake zargi da kashe matafiya musulmai.
Wannan ya zo ne bayan da wasu ‘yan ta’adda suka yi wa matafiya kisan gilla a wani yankin jahar ta Filato.
A halin yanzu, rundunar ta ce tana kan bincike don tabbatar da adalci da kuma mika su ga inda ya dace.
Jos, Filato – Rundunar tsaro ta musamman, Operation Safe Haven (OPSH) a jahar Filato, ta cafke wasu mutane 12 da ake zargi da aikata kashe-kashe da safiyar Asabar a kan hanyar Rukuba ta karamar hukumar Jos ta Arewa a jahar, in ji rahoton PM News.
Read Also:
OPSH ne ke da alhakin wanzar da zaman lafiya a fadin jahar Filato da kewaye. Manjo Ishaku Takwa, jami’in yada labarai na rundunar, ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa ranar Asabar a garin Jos.
Wani yankin sanarwar ya shaida cewa:
“Zuwa yanzu, an cafke mutane 12 da ake zargi da hannu a cikin lamarin kuma sojoji na kan bin sawun wasu, wadanda ke da hannu a wannan mummunan aikin.
“Wadanda aka kama a halin yanzu suna tsare don amsa tambayoyi.”
Takwa ya ce Kwamandan rundunar, Maj-Gen. Ibrahim Ali, ya bukaci jama’a da su ba da sahihan bayanai masu sahihanci wadanda za su kai ga cafke sauran wadanda ake zargi, a halin yanzu.
Ya ce, kwamandan ya kuma yi kira ga mazauna yankin da su kwantar da hankulansu, su kasance masu bin doka da oda kuma su ci gaba da ayyukansu ba tare da wani fargaba ba.
Hakazalika, ya ce jami’an tsaro sun kara kaimi wajen sintiri a cikin garin Jos don wanzar da zaman lafiya da tsaro.