Najeriya bata Cimma Komai ba a Cikin Shekaru 40 – Muhammadu Sanusi II

 

Tsohon sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya bayyana yadda Najeriya ta gagara cimma komai cikin shekaru 40.

A cewarsa, maganganun da yake a baya, an dauka yana sukar lamirin abubuwan da ke faruwa ne, amma yanzu ga gaskiyar batu.

Ya kuma roki ‘yan Najeriya da a tashi tsaye wajen ganin an inganta tattalin arzikin kasar nan ba babba ba yaro.

Kaduna – Alhaji Muhammad Sanusi, tsohon Sarkin Kano, ya ce Najeriya ba ta samu wani ci gaba ba cikin shekaru 40, tun mulkin shugaban kasa Shagari, Daily Trust ta ruwaito.

Sanusi ya fadi haka ne a wani taron tattaunawa na murnar cikarsa shekaru 60 a duniya da aka gabatar jiya Asabar 14 ga watan Agusta, 2021.

Tsohon Gwamnan na Babban Bankin Najeriya (CBN) ya ce akwai bukatar ci gaba a fannin tattalin arzikin kasa.

Na biya farashin fadin gaskiya.

Ya ce duk da ya biya farashi saboda fadin gaskiya, ‘yan Najeriya sune suka biya ainihin farashi ta bangaren zama “cikin talauci, rashin tsaro, da hauhawar farashin kaya ”.

A cewarsa:

“Lokacin da kuke cikin al’ummar da ba daidai take ba, ba za ki iya zama mai daidaita abubuwa ba, saboda idan duk kun daidaita, abubuwa ba za su canza ba.”

“Shekaru da yawa da suka gabata, lokacin da nake kururuwa akan biliyoyin da ake kashewa akan tallafin man fetur, na tuna an yi yunkurin kai hari gidana a Kano.

Sannan ina CBN. Ina muke a yau?

Muna fuskantar gaskiya – cewa tallafin mai ba zai dawwama ba.

Legit Hausa ta tattaro daga rahoton Daily Trust cewa, Sanusi ya kara da jan hankali cewa:

“Kira na makiyi ko mai sukar lamiri ba zai sa wadannan hujjojin su tafi ba. Don haka, duk inda muka je, dole ne mu fuskanci wannan gaskiyar.

“Na yi kokarin kada in fadi da yawa, ba wai saboda babu abin da zan fadi ko saboda ina jin tsoron magana ba.

“Dalilin da yasa ban yi magana da yawa ba a cikin shekaru biyu da suka gabata shine saboda, ba ma sai na sake cewa komai ba, saboda duk abubuwan da muke gargadin su sun bayyana.

“A cewar Bankin Duniya, ina muke a 2019?

A wannan adadin, a cikin shekaru biyu masu zuwa, dangane da daidaiton ikon siye, matsakaicin kudin shiga na dan Najeriya zai koma yadda yake a da tun 1980 a karkashin mulkin Shehu Shagari.

“Wannan yana nufin a cikin shekaru 40, ba mu sami ci gaba ba; Shekaru 40 sun lalace a banza.

Gwamna Aminu Tambuwal na jahar Sokoto; tsohon Mataimakin Gwamnan CBN, Kingsley Moghalu; mataimakin gwamnan jahar Kaduna, Dakta Hadiza Balarabe; Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmad Nuhu Bamali; duk sun halarci taron tattaunawar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here