Rundunar Sojojin Najeriya Sun Bayyana Cewa Sun Ceto ƙarin Mutane 7 Daga Cikin Waɗanda Harin Jos Ya Rutsa da Su

 

Rundunar sojojin Operation Safe Haven sun sake ceto karin mutum 7 daga cikin waɗanda harin Jos ya rutsa da su.

Sojojin sun bayyana cewa sun kai mutanen wani wuri mai tsaro domin cigaba da duba lafiyar su.

Wannan ya biyo bayan wani hari da aka kaiwa matafiya da suka dawo daga zikirin shekara-shekara a Bauchi.

Plateau – Sojojin Najeriya a jahar Filato na Opertaion Safe Haven sun bayyana cewa sun ceto ƙarin mutum 7 daga cikin waɗanda harin Jos ya rutsa da su.

Wannan na zuwa ne bayan wani hari da aka kaiwa matafiya a kan hanyar Rukuba, karamar hukumar Jos ta arewa, jahar Filato.

Punch ta ruwaito cewa da farko sojojin sun kubutar da mutum 12 yayin harin, wanda yayi sanadiyyar mutuwar aƙalla mutum 25, wasu da dama suka jikkata.

Mutanen sun dawo daga zikiri a Bauchi

Rahotanni sun nuna cewa matafiyan sun dawo ne daga zikirin shekara-shekara a jahar Bauchi kuma suna kan hanyar zuwa Ikare jahar Ondo.

A wata sanarwa da kakakin rundunar sojin Operation Safe Haven, Manjo Ishaku Takwa, ya fitar yau Lahadi, yace waɗanda aka ceto ɗin an kai su wani wuri mai tsaro domin kulawa da lafiyarsu.

Sanarwar tace:

“A yau Lahadi sojojin Operation Safe Haven sun sake ceto karin mutum 7 daga cikin matafiyan da aka kaiwa hari a Rukuba jiya Asabar.”

“A halin yanzun sojojin sun kai waɗanda suka ceto ɗin wani wuri mai tsaro domin cigaba da kula da lafiyarsu.”

“Hakanan kuma sojojin na cigaba da binciken gano tare da ceto sauran waɗanda suka bata yayin harin.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here