An Kama Mutanen da Sukai Garkuwa da Matar Kwamishina a Jahar Benue
An cafke wasu mutane da suka yi awon gaba da matar kwamishina a jahar Benue, an kuma garkamesu.
An kame su da muggan makamai da sauran kayayyakin aikata laifuka bayan samun bayanan sirri.
An maka su a kotu, inda kotun ta ba da umarnin ci gaba da adana su a gidan gyaran hali zuwa lokacin da za a yi shari’a.
Benue – Wata kotun majistare da ke Makurdi ta bayar da umurnin a ci gaba da tsare wasu mutane takwas a gidan yarin jahar bisa zarginsu da yin garkuwa da Ann Unenge, matar kwamishinan filaye, bincike da ma’adanai na jahar Benue.
Wadanda ake zargin sune Samuel Ogbodo, Chidi Anekwe, Monday Anyigor, John Igwe, John Nwoke, Mathias Odoh, Matthew Eze da Iorhemen Yagba, The Cable ta rawaito.
An tuhume su da laifin hada baki, fashi da makami da ta’addanci, wadanda laifuka ne da suka saba da tanadin sassan daban-daban na dokoki na musamman na jahar Benue.
Read Also:
Adah Odeh, alkalin kotun, ya ba da umurnin a ci gaba da tsare su a cibiyar gyaran hali ta tarraya, har zuwa lokacin da za a yankje shawara kan shari’ar.
Tun da farko, Lauyan ‘yan sanda Rachael Mchiave, ta shaida wa kotun cewa an samu karar a sashin binciken manyan laifuka na jahar (SCID) da ke Makurdi, ta hanyar wasika mai lamba CJ: 4161/BNS/JTF/OPZ/VOL. 1/440 a ranar 2 ga Agusta.
Mchiave ta ce jami’an rundunar hadin gwiwa (JTF), karkashin jagorancin Usman Dalamin, dake aiki da rahoton bayanan sirri, sun fatattaki wata tawaga da ake zargin ta sace matar kwamishinan da direbanta a ranar 29 ga watan Yuli.
Ta ce sun nemi kudin fansa Naira miliyan 51.
Mai gabatar da kara ya kuma yi zargin cewa an kwato bindiga kirar AK-47 guda daya mai lamba 5006971, magazine guda biyu dauke da harsasai 28, harsasai guda biyu, bindigar gida da layu daga hannun wadanda ake zargin.
Ta ce ana ci gaba da gudanar da bincike a kan lamarin tare da rokon kotun da ta dage sauraron karar.
An daga sauraran karar zuwa ranar 12 ga watan Oktoba don ci gaba da magana.