An Kama Magoya Bayan Arsenal Kan Murnar Nasarar Doke Abokiyar Hamayyarta Man United
Aƙalla magoya bayan ƙungiyar Arsenal takwas aka kama a birnin Jinja na kasar Uganda, sakamakon murnar nasarar da ƙungiyar ta yi kan babbar abokiyar hamayyarta Manchester a wasan Premier League da suka buga ranar Lahadi.
Magoya bayan – waɗanda ke sanye da jajayen rigunan ƙungiyar – na riƙe da wani abu da ke alamta kofin Premier.
Read Also:
‘Yan sanda sun ce mutanen ba su da izinin gudanar da gangamin, kuma yin hakan laifi ne a ƙasar.
Arsenal ta samu nasara a kan abokiyar hamayyarta Manchester United da ci 3-2 a wasan na ranar lahadi.
Sakamakon ya bai wa ƙungiyar tazarar maki biyar a saman teburin Premier, lamarin da ya bai wa magoya bayanta a faɗin duniya ƙwarin gwiwwar ɗaukar kofin Premier karon farko cikin shekara 19.
‘Yan sanda sun kama magoya bayan – waɗanda ke cikin jerin gwanon motoci ranar Litin da safe – inda ɗaya daga cikinsu ke riƙe da kofin da suka haɗa kuɗi suka saya a wani shago a ƙasar.