EFCC ta Kama Matar Gwamnan Kano: Gwamnatin Jahar ta yi Martani Kan Batun

 

Gwamnatin jahar Kano ta yi martani kan batun kame matar gwamnan jahar Kano, Hajiya Hafsat.

Ganduje – Gwamnatin Kano ta ce, ba a kame ta ko tsare ta ba tana nan tana ci gaba da ayyukanta da suka dace.

Gwamnatin ta kuma bayyana cewa, ya kamata mutane su ke gudun jita-jita da ake yadawa a kafafen sada zumunta.

Kano – Gwamnatin Jahar Kano ta mayar da martani kan rahotannin da ke cewa hukumar EFCC ta cafke matar Gwamna Abdullahi Ganduje, Farfesa Hafsat Ganduje, tana mai cewa labarai ne kawai wadanda ‘yan adawa ke daukar nauyin ta.

A cewar wata sanarwa, Kwamishinan Yada Labarai na jahar Kano, Malam Muhammad Garba, ya nuna nadama kan jita-jitar, inda ya kara da cewa ba za a iya bin diddigin labarin da ba shi da tushe daga wata tushe mai kyauta ba kamar dai hukumar EFCC kanta.

Ya bayyana cewa abin takaici, an yada labaran karya a kafafen sada zumunta ba tare da tabbatarwa daga gwamnati ko hukumar hana almundahanar ba, SaharaReporter ta rawaito.

Garba ya ce:

“Ba a kama matar gwamnan ko aka tsare ta ba kuma a halin yanzu tana nan tana sauke nauyin da ke kanta.”

Kwamishinan ya yi kira ga mutanen kirki na jihar da su yi watsi da jita-jitar, inda ya bukace su da su kwantar da hankalinsu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here