Bayan Mata Ciki: An Kama Saurayin da ya Kashe Budurwasa a Adamawa
Rundunar ‘yan sanda a jahar Adamawa sun cafke wasu matasa da laifin kashe wata budurwa.
Rahoto ya bayyana yadda matasan suka hada kai wajen kashe wata budurwa Franca Elisha.
Bayan tabbatar da ta mutu, sun kwashi gawarta suka binne a wani dan karamin rami mara zurfi.
Adamawa – Rundunar ‘yan sandan jahar Adamawa ta gurfanar da wani dalibin Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Tarayya da ke Mubi, Mumuni Abubakar, bisa zargin kashe budurwarsa mai juna biyu, Franca Elisha, tare da binne gawarta a cikin rami mara zurfi.
Rundunar ta kuma gurfanar da wasu abokansa biyu, Huzaifa Shuaibu da Rabiu Adamu, saboda rawar da suka taka dumu-dumu a lamarin, Punch ta rawaito.
Franca Elisha, dalibar Diploma a Sashen Kimiyyar Laburare a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Tarayya dake Mubi, an binne ta a cikin rami mara zurfi bayan kokarin zubar da ciki da ta yi ya faskara.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Suleiman Nguroje, ya ce korafin da iyayen marigayiyar suka yi game da inda take ya kai ga binciken da ya gano yanayin da ke tattare da mutuwar ta.
Mumuni Abubakar, mazaunin Unguwar Sanda dake karamar hukumar Yola ta Arewa, ana zargin ya dirkawa Franca ciki, kuma da ta sanar da shi, sai ya dage cewa lallai ne ta cire cikin.
Rahoton Farko na ‘yan sanda ya ce:
“Ya kai marigayiyar dakinsa da ke unguwar dalibai a bayan jami’ar jahar don zubar da cikin a asirce a ranar 6 ga Agusta, 2021.
“Don samun nasarar aiwatar da shirin zubar da cikin, wanda ake tuhuma ya gayyaci abokinsa kuma dalibin Kwalejin Kiwon Lafiya da Fasaha dake Mubi, Huzaifa Shuaibu, wanda ya yi amfani da miyagun kwayoyi da allurai don cire dan a cikin mahaifar Franca.”
An yi zargin allurar ta jawo wa Franca wani nau’in tashin hankali, yayin da ta mutu.
Mumuni, a cikin bayanin furucinsa, ya ce budurwar tasa daga baya ta farfado.
A cewarsa:
“Amma don cimma zubat da cikin, Shuaibu ya sake tsikara mata allurar bayan ta farfado.
“Abin takaici, ta suma a karo na biyu kuma ba ta farfado ba; daga baya ta mutu.
”Wadanda ake zargin sun gayyaci Adamu, wani abokinsu, domin ya taimaka wajen kawar da gawar Franca.
Abubakar ya ce:
“Mun dauki gawar muka binne a cikin rami mara zurfi tare da wayar hannu da katin shaidar zama dan kasa, sannan muka ci gaba da rayuwarmu ta yau da kullum, muna yin kamar ba abin da ya faru.”
 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here