An Kara Daga Shari’ar El-Zazzaky Zuwa 2021
A ranar Laraba ne babbar kotun jihar Kaduna ta sake zama domin sauraron shari’ar Shugaban ƙungiyar Shi’a, Sheik Ibrahim El-Zakzaky, da matarsa, Zeenat.
Bayan sauraron shaida daga wasu manyan sojoji guda biyu; Janaral da Kanal, kotun ta gada cibaga da suraron shari’ar zuwa ranar Alhamis.
Alkalin kotun, Jastis Gideon Kurada, ya sake daga cigaba da sauraron karar zuwa watan Janairu na shekarar 2021.
A ranar Alhamis ne wata babbar kotun jihar Kaduna ta sake daga sauraron shari’ar shugaban kungiyar Shi’a, Sheikh Ibrahim El-zakzaky, zuwa ranar 25 ga watan Janairu na shekarar 2021.
Alkalin kotun, Jastis Gideon Kurada, ya daga Shari’ar ne bayan shaidu hudu sun bayar da shaida a zaman kotun na ranar Alhamis.
Read Also:
Gwamnatin jihar Kaduna ta gurfanar da El-zakzaky da matarsa, Zeenat, bisa tuhuma guda takwas da suka hada da zargin haddasa rashin rayuka da taro ba bisa ka’ida ba da hana jama’a zaman lafiya da sauransu.
A ranar 29 ga watan Satumba ne El-zakzaky da matarsa suka ce basu aikata laifukan da ake zarginsu dasu ba.
Wani Manjo Janaral da Kanal ɗin soji sun bada shaidarsu a gaban alƙali Kurada akan shari’ar El-Zakzaky da matarsa Zeenat a ranar Laraba.
Jagoran lauyoyi masu kare Zakzaky, Femi Falana, a lokacin da yake magana da manema labarai bayan zaman kotun, ya ce an ɗage shari’ar zuwa 19 ga Nuwamba, 2020 don cigaba da sauraron ƙarar.
Da ya ke magana da manema labarai ranar Alhamis bayan zaman kotun, Falana ya ce daga cikin wadanda suka bayar da shaida a ranar Alhamis akwai wani tsohon darekta a hukumar tsaro ta farin kaya (DSS).