Bisa Kuskure: Gwamnatin Tarayya Zata Karbo Kudaden da ta Biya Likitoci 588

 

Gwamnatin tarayya za ta karbo miliyoyin nairorin da ta yi kuskuren biyan likitoci 588 da ke fadin kasar nan.

Ministan kwadago da ayyuka, Chris Ngige ne bayyana hakan yayin amsa tambayoyin maneman labaran gidan gwamnati a Abuja.

Ya bayyana cewa an biya likitocin bisa kuskure ne maimakon wasu bangaren likitocin na daban yanzu haka wasunsu sun fara mayar da kudaden.

FCT, Abuja – Gwamnatin tarayya za ta amso miliyoyin nairorin da ta biya likitoci 588 da ke fadin kasar nan bisa kuskure.

Daily Trust ta rawaito cewa, ministan kwadago da ayyuka, Sanata Chris Ngige ne ya bayyana hakan yayin amsa tambayoyin manema labaran gidan gwamnati a Abuja.

Ya bayyana yadda kudaden suka shiga asusan likitoci na daban maimakon na likitoci masu neman kwarewa.

A cewar sa, bayan shugabannin likitocin asibitocin Najeriya sun zauna sun bi daki-daki ne suka tattaro sunaye 8000 na likitocin, Daily Trust ta wallafa.

Ministan ya bayyana yadda wasu daga cikin likitocin suka fara maido da kudaden yayin da ake kokarin ganin an tattaro sauran kudaden.

Ya bayyana yadda rashin karashe biyan kudade yake kara janyo gwamnati ta na daukar lokaci wurin biyan likitoci masu neman kwarewa.

“Mun yi bincike karo na farko kuma yanzu haka makarantun horar da likitoci sun bayyana sunayen su, masu neman kwarewa. An tattaro sunayen wurin 8000 kuma yanzu haka ma’aikatar lafiya ta na karasa bincike a kan su.

“Kungiyar likitoci masu neman kwarewa ta kowanne makarantar likitoci ta na aiki da shugaban likitocin wurin ganin sun tattara duk sunayen su.

“Wannan dalilin ne ya janyo bacin lokaci wurin biyan likitoci masu neman kwarewa kudaden su wanda ya kamata ma’aikatar kudi ta ke kokarin yi,” a cewarsa.

“Sannan ya kara da bayyana yadda gwamnati za ta bi dokar ‘babu aiki babu biya’ saboda kusan ko wacce kasa ta na aiwatar da hakan, yadda ya auku a 2020. A 2020, ba a binciki sunayen da aka kawo ba ne da kyau.

Sannan ya kara da bayyana yadda gwamnati za ta bi dokar ‘babu aiki babu biya’ saboda kusan ko wacce kasa ta na aiwatar da hakan.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here