An Samu ƙarancin Masu Kaɗa ƙuri’a a Kaduna
Rahotonni daga jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya sun ce an samu ƙarancin fitowar masu kaɗa ƙuri’a a zaɓen gwamna da na ƴan majalisar dokoki da ake gudanarwa a jihar.
Bayanai sun nuna cewa tun misalin ƙarfe 8:30 na safe aka fara kaɗa ƙuri’a a wasu sassan birnin.
Read Also:
A mafi yawan rumfunan zaɓen da BBC ta ziyarta a cikin birnin Kaduna an ga ƙarancin fitowar mutane domin kaɗa ƙuri’a, ba kamar yadda aka gani a zaɓen shugaban ƙasar da ya gabata ba, inda mutane da dama suka fito.
Wani mai kaɗa ƙuri’a mai suna Malam Baba ya shaida wa BBC cewa a mazaɓarsa da ke unguwar Kawo mutane ƙalilan ne suka fito zaɓe.
Ya kuma ce babu mata sosai a rumfar zaɓen nasa.
A sassan ƙasar da dama dai rahotonni na cewa mutane ba su fito zaɓen ba kamar yadda suka fita zaɓen shugaban ƙasa.