Ta da Hankali: Ƴan Sanda Sun Kama Shugaban Kano Line

Rahotannin daga jihar Kano na cewa rundunar ƴan sanda jihar ta kama shugaban kamfanin sufuri na jihar Kano Line bisa zargin tayar da hatsaniya a lokacin zaɓe.

Rundunar ta wallafa a shafinta na Facebook cewa ta kama mutane uku a unguwar Gwammaja Ƴan Ƙosai, kuma mutanen suna zaune ne a bayan motar ƴan sanda.

Daya daga cikin wadanda aka kama din dai shi ne shugaban Kano Line Bashir Nasir Aliko.

Shugaban ɗa ne ga Nasiru Aliko Ƙoki, daya daga dattawan jam’iyyar APC a Kano, kuma na hannun damar gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje.
Kawo yanzu dai babu wani ƙarin bayani daga rundunar ƴan sanda kio jam’iyyar APC .

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here