Murabus: Tawagar Wakilan ƙungiyar Kasashen Nahiyar Africa ta Gana da Shugaban Kasar Mali
Tawagar wakilan ƙungiyar kasashen nahiyar Afirca ECOWAS ta gana da hamɓararren shugaban Mali da Firam minista. No
Shugaban Mali da Firam minista sun shaida wa wakilan ECOWAS ɗin sun yi murabus daga kan muƙamansu.
Wata majiya mai ƙarfi ta bayyana cewa sojoji ne suka tilasta musu yin murabus ɗin bawai don son ransu bane.
Tawagar wakilan ƙungiyar ƙasashen nahiyarAfirca ECOWAS ta gana da tsohon shugaban ƙasar Mali, Bah Ndaw, da sojoji suka kifar tare da Firaminista.
Read Also:
Tawagar wakilan ƙarƙashin jagorancin Dr. Goodluck Ebele Jonathan, tsohon shugaban ƙasar Najeriya ta gana da shugaban ne biyo bayan hamɓarar da shi da sojoji suka yi ranar Litinin..
A lokacin ganawar tasu, shugaban Mali da Firaminista sun bayyana aje muƙamansu ga wakilan ECOWAS ɗin.
Rahoton da BBC ta ruwaito ya nuna cewa sojoji ne suka tilasta wa shuwagabannin biyu dole su sauka daga kan muƙamansu.
Kanal Assimi Goita, Sojan da ya shugaban ci hamɓarar da gwamnatin ƙasar a shekarar da ta gaba ta ya bada sanarwar tsige shugaban ƙasa da Firaminista ranar Talata.
Kanal ɗin yace yana zargin su da da naɗa sabbin minitoci a gwamnatin rikon ƙwarya ba tare da tuntuɓar ɓangaren sojojin ba.
A halin yanzu ƙungiyar ECOWAS da takwararta da Turai na duba yuwuwar sanya takunkumi ga sojojin da suka jagoranci juyin mulkin.
Ana sa ran, yau kwamitin tsaro na majalisar ɗinkin duniya zai zauna ya tattauna kan rikicin siyasar ƙasar Mali.