Shugaba Buhari ya Nada Farouk Yahaya a Matsayin Sabon Shugaban Hafsan Sojojin Kasa

 

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Farouk Yahaya a matsayin sabon shugaban hafsan sojojin kasa.

Farouk Yahaya mai mukamin Manjo Janar ya maye gurbin marigayi Laftanal Janar Ibrahim Attahiru da ya rasu a hatsarin jirgin sama.

Kafin nadin nan, shine babban kwamandan Div 1 kuma shugaban rundunar Operation Hadin kai dake yaki da ta’addanci a arewa maso gabas .

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Farouk Yahaya a matsayin shugaban dakarun sojojin kasa na Najeriya.

Yahaya, mai mukamin manjo janar zai maye gurbin marigayi Attahiru Ibrahim a take.

Kafin nadinsa, Yahaya shine babban kwamandan Div 1 na rundunar sojin kasa ta Najeriya.

Kamar yadda hedkwatar dakarun sojojin kasa ta Najeriya ta wallafa a shafinta na Twitter, ta sanar da cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Manjo Janar Farouk Yahaya a matsayin sabon shugaban sojojin kasa.

“Babban kwamandan dakarun sojojin Najeriya, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Manjo Janar Farouk Yahaya a matsayin sabon shugaban hafsin sojojin kasa.

“Kafin nadinsa, Manjo Janar Yahaya shine babban kwamandan Div 1 ta dakarun sojin kasa kuma shine kwamandan rundunar Operation Hadin Kai dake yaki da ta’addanci a yankin arewa maso gabas,” takardar tace.

Manjo Janar Farouk Yahaya ya maye gurbin marigayi Laftanal Janar Ibrahim Attahiru, wanda hatsarin jirgin saman ya ritsa dashi a ranar Juma’a da ta gabata a garin Kaduna.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here