ƙasashen da Suka Kwashe Mutanensu Daga Sudan Zuwa Yanzu
Daidai lokacin da yaƙin da ake gwabzawa ya shiga mako na biyu, ƙasashen waje sun fara ƙoƙarin kwashe jami’an diflomasiyyarsu da kuma’yan ƙasashensu a ƙarshen makon da ya wuce.
Ga taƙaitaccen bayani kan abin ya faru zuwa yanzu:
Amurka da Kanada da Burtaniya sun ba da sanarwa a ranar Lahadi cewa sun kwashe jami’an diflomasiyyarsu zuwa wajen ƙasar ta Sudan
Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya tabbatar da cewa jami’an ƙasarsa sun yi aikin kwashe Faransawa a ranar Lahad da Litinin, inda suka fitar da ‘yan Faransa 388 da jami’an diflomasiyyar ƙasar daga Sudan
Haka zalika, an kwashe wasu mutanen ƙasar Holland su ƙalilan daga birnin Khartoum a jiragen saman Faransa
Rundunar sojojin Jamus ta ce jiragen sama guda uku a karon farko sun bar Sudan inda suka nufi Jordan da mutum 101 a ciki
Read Also:
Italiya da Sifaniya sun kwashe mutanensu – Jami’an ofishin jakadancin Sifaniya sun ƙunshi ‘yan ƙasar Argentina da Colombia da Ireland da Portugal da Poland da Mexico da Venezuela da Sudan.
Turkey- wata muhimmiyar mai ba da gudunmawa cikin harkokin Sudan – ta tattara mutum 640 a cikin motocin bas-bas 13 don kwashe su ta hanyar titin mota – ƙarin wasu 500 kuma sun taru a wata cibiyar kwashe ‘yan ƙasashen waje. Ofishin jakadancin Turkey na ƙunshe da ‘yan ƙasashen Azerbaijan da Japan da China da Mexico da kuma Yemen
Mutanen ƙasashen Turai fiye da 1,000 aka kashe daga Sudan, kamar yadda babban jami’in kula da manufar hulda da ƙasashen ƙungiyar chief Josep Borrell ya ce a ranar Litinin, musammam ma ya gode wa Faransa kan aikin da ta yi.
Mutane fiye da 150 ne akasari daga ƙasashen yankin Gulf da Masar da Pakistan da Kanada aka kwashe ta ruwa zuwa tashar tekun Jeddah a ƙasar Saudiyya.