Kasashe Masu Tasowa Sun fi Sauran Jin Radadin Bannar da corona ta yi – IMF
Asusun bada lamuni na duniya ya yi gargadin cewa akwai rashin tabbas game da farfadowar tattalin arzikin duniya bayan illar da annobar corona ta yi masa.
IMF ya ce kasashe masu tasowa sun fi sauran jin radadin bannar da coronar ta yi.
Asusun ba da lamunin ya ce tattalin arzikin kasashen masu tasowa na fuskantar cikas ne sakamakon karancin rigakafin cutar corona.
Hakama IMF ya ce jinkirin da ake fuskanta wajen shigo da abinci da kayayyaki ya taimaka wajen samun karuwar hauhawar farashi, kuma wannan ya sa an rage hasashen bunkasar tattalin arzikin a bana.
Asusun ya kuma ce hauhawar farashin kayayyaki zai cigaba da kasancewa a yan watanni masu zuwa, yayin da ake ci gaba da samun rashin daidaito a alkaluman kayan da ake samarwa da kuma bukatarsu, inda ya buga misali da tsadar makamashi da ake fuskanta.
 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here