An Kashe Jiga-jigan ‘Yan Ta’addan Boko Haram a Borno

Gungun ‘yan ta’addan ISWAP sun kai wa ‘yan ta’addan Boko Haram hari a wani yankin jahar Borno.

Rahoto ya ce an hallaka wasu jiga-jigai daga cikin kwamandojin Boko Haram a kwanton baunar na ISWAP.

Hakazalika, wasu 15 daga cikin mambobin kungiyar duk su ma sun hallaka a harin na ranar Lahadi.

Borno – Jaridar PRNigeria ta ruwaito cewa an kashe manyan jiga-jigan kungiyar Boko Haram guda biyu, Amir Modou Marte da Amir Moustapha Baga .

An kawar da su ne a wani kwanton bauna da mayakan abokan hamayyarsu na ISWAP suka yi a ranar Lahadi 24 ga watan Oktoba.

An tattaro cewa wasu ‘yan ta’adda 15 na daga cikin wadanda kungiyar Boko Haram ta kashe a lokacin kwanton baunar da suka yi a Toumboun Gadura’a.

Karin bayani na nan tafe…

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here