An Kashe Sojoji 18 a Harin Satar Shanu a Sudan ta Kudu
Akalla mutum 25 wadanda suka hada da sojoji aka kashe a lokacin wani harin karbe shanu da aka kai a jihar Warrap da ke fama da rikici a yankin tsakiyar Sudan ta Kudu, kamar yadda jami’ai suka sheda wa BBC.
Jimilla an kashe sojoji 18 da farar-hula bakwai a lokacin rikicin da matasa dauke da muggan makamai, in ji ministan yada labarai na jihar Warrap, Ring Deng.
Daga cikin mutanen da suka rasa ransu akwai wani babban hafsan soja da kuma wani tsohon kwamishina, kamar yadda BBC ta fahimta.
Read Also:
Haka kuma an raunata sojoji bakwai da farar-hula shida a lokacin rikicin.
Ana fargabar cewa yawan wadanda suka rasa ransu zai iya kaiwa 65, kamar yadda jaridar Sudan Post ta ruwaito, amma kuma Mista Ring ya musanta hakan.
Ya ce rikicin ya barke ne sakamakon rashin fahimta da aka samu a lokacin da sojoji suka yi kokarin karbo shanun da aka sace daga matasan.
Harin satar shanu da ramuwar gayya sun yi sanadiyyar kisan dubban mutane a Sudan ta Kudu tun bayan da kasar ta samu ‘yancin kanta a 2011.
Har yanzu kasar na fama da matsalar tsaro duk da kafa gwamnatin hadin kan kasa a watan Fabrairu na 2020.