Tsananin Zafi da Kishirwa ya yi Sanadiyyar Kashe Mutane 46 a Cikin Babbar Mota a Amurka

An samu mutum akalla 46 da suka mutu a wata babbar mota da aka yi watsi da ita a birnin San Antonio na jihar Texas a Amurka.

Wani jami’in kwana-kwana ya ce mutane akalla 16 wadanda suka hada da yara hudu aka garzaya da su asibiti.

Alamu sun nun cewa wadanda suka tsira da ransu suna fama da tsananin zafi da kuma gajiya.

Birnin San Antonio, wanda ke da nisan kilomita 250 (mil 150) daga iyakar Amurka da Mexico, babbar hanya ce ta satar shigar da mutane Amurka.

Masu safarar mutane kan yi amfani da manyan motoci wajen daukar bakin haure idan suka hadu da su a kauyuka, idan har sun tsallaka zuwa cikin Amurka.

Jami’ai sun ce babbar motar wadda direbanta ya gudu ya bar ta a wurin, ba ta da na’urar sanyaya (daki) sundukinta wato iyakwandishin sannan kuma ba ruwan sha a cikinta

Zafin rana a San Antonio a lokacin bazara a ranar Litinin ya kai maki 39.4C (103F), saboda haka ana ganin mutanen sun mutu ne saboda tsananin zafi da kishirwa.

Ministan Waje na Mexico, Marcelo Ebrard, ya ce akwai ‘yan Guatemalan biyu daga cikin wadanda aka garzaya da su asibiti.

Zuwa wannan lokacin ba a tantance ainahin kasar sauran mutanen ba.

Ana tsare da mutum uku bisa zargi da hannu a lamarin, yayin da aka mika bincike ga jami’an tarayya.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here