Saudiyya ta Bukaci ‘Yan Kasar su Fara Duba Sabon Watan Dhul Hijjah Ranar Labara

 

Hukumomi a Saudiyya sun bukaci ‘yan kasar su soma duba sabon watan Dhul Hijjah na shekarar Musulunci ta 1443 ranar Laraba da almuru.

Wani sako da shafin Haramain Sharifain ya wallafa a Tuwita ya nemi ‘yan kasar su kai rahoton ganin watan idan sun gan shi.

Tuni dai mahajjata suke ci gaba da isa kasar ta Saudiyya domin gudanar da ayyukan ibada.

Mahajjata miliyan daya ne daga ciki da wajen kasar za su gudanar da ayyukan ibada a bana.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here