Hukuncin da Kotu ta Yanke wa Wadanda Suka Kashe Zabiya a Malawi

 

Wata kotu a Malawi ta yanke hukuncin daurin rai da rai tare da aiki mai tsanani a kan wasu mutane biyar saboda samunsu da laifin kisan wani zabiya a shekara ta 2018.

An gano gawar mutumin ne mai suna MacDonald Masambuka, a wani dan rami da aka binne ta, bayan ya yi makonni ba a gan shi ba.

Wadanda aka yi wa hukuncin a birnin Blantyre, sun hada da wani limamin cocin Katolika da dan sanda da kuma wani dan uwan mamacin.

A watan Afrilu ne kotun ta same su da laifin kisan gillar.

Ana danganta kisan zabiya da tsafi, inda bokaye da wasu masu maganin gargajiya ke karyar cewa ana amfani da sassan jikinsu domin samun nasara ko dukiya.

Hukumomin kasar ta malawi sun ce tun shekarar 2014 an kai wa mutane masu larurar zabiya har 170 hari, da suka hada da sama da 20 da aka kashe.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here