‘Yan Arewa: An Kashe ‘Yan Kasuwa 7 a Jahar Imo

 

An shiga cikin yanayin tashin hankali a jahar Imo bayan kisan wasu yan kasuwa 7 ‘yan Arewa da aka yi a cikin kwana biyu.

Shaidun gani da ido sun tabbatar a aukuwar lamarin, kuma sun ce mutanen da aka kashe sun daɗe suna rayuwa a yankin ba tare da wata matsala ba.

Sai dai rahotanni sun bayyana cewa waɗanda suka aikata wannan mummunan aikin baƙi ne don ba’a gane ko suwaye ba Ana cikin yanayin ɗar-ɗar da da tashin hankali a jahar Imo bayan wani kisa da akai ma yan kasuwa 7 ‘yan arewa a jahar.

Rahoton jaridar Dailytrust ya bayyana cewa an kashe mutanen ne a harbi daban-daban a garin Orlu da Umuaka dake ƙaramar hukumar Njaba tsakanin ranar Jumu’a da Asabar.

Ya kuma ƙara da cewa, a yanayi irin wancan, yan bindigan suka sake kawo hari a kasuwar Umuaka, inda suka sake buɗewa hausawa yan kasuwa wuta.

Abdulƙadir ya ce, yanzu yan kasuwa hausawa na rayuwa cikin tsoro a garin Orlu, ya ƙara da cewa wasu ma har sun bar garin zuwa Owerri.

A bayaninsa Abdulƙadir yace:

“Maganar gaskiya wannan abun ya fara ne tun biyu ga wannan watan, an kira ni a waya an faɗa mun wasu yan bindiga a motar Sienna sun kashe masu siyarda suya uku.”

“Muna ƙoƙari akan wannan lamarin sai kuma aka sace kirana akace an sake kashe wasu mutum huɗu.”

Wakilin Dailytrust ya gano cewa an ɗauki gawarwakin waɗanda aka kashe an tafi dasu Owerri don yi musu jana’iza.

Babban mai baiwa gwamnan jahar shawara kan al’amuran mutanen arewa, Hon. Sulaiman Ibrahim Sulaiman, ya ce gwamnatin jahar da dukkan hukumomin tsaron sun shiga cikin lamarin.

Ya yin da yake kira da akwantar da hankulla, Sulaiman ya ce gwamnan jahar ya damu d lamarin da ya faru. Duk wani yunƙuri na jin ta bakin mai magana da yawun hukumar ‘yan sandan jahar ya ci tura, saboda an kasa samun wayarshi.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here