Kasuwanci Sun Tsira Duk da Annobar COVID-19 – Yemi Osinbajo
Yemi Osinbajo ya bayyana yadda gwamnatinsu ta tsare tattalin arzikin Najeriya.
Mataimakin shugaban kasa yace kasuwanci sun tsira duk da annobar COVID-19.
Farfesa Osinbajo yake cewa gwamnatin tarayyar ta hana kasuwanci tashi a aiki.
Abuja – Mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, yace tsare-tsaren tattalin arzikin gwamnatin nan sun ceci sana’ar mutane miliyan daya daga durkushe wa.
Punch tace Farfesa Yemi Osinbajo yake cewa tsare-tsaren sun hana a rufe kananan kasuwanci 150, 000 a lokacin da annobar cutar COVID-19 ta addabi kasashe.
Mataimakin shugaban kasar yace shirye-shiryen gwamnatin Muhammadu Buhari sun yi maganin talauci, suka samar da ayyukan yi, suka inganta rayuwa.
Farfesa Osinbajo ya yi wannan bayani a ranar Talata, 28 ga watan Satumba, 2021, wajen wani zama da majalisar dinkin Duniya ta shirya ta kafar yanar gizo.
Read Also:
Laolu Akande ya fitar da jawabin da mataimakin shugaban Najeriyar ya gabatar a birnin Abuja.
Yemi Osinbajo ya gabatar da jawabi mai taken ‘Why social protection schemes are crucial’ domin ya yi bayanin fa’idar manufofin da gwamnatin APC ta kirkiro.
A cewar Osibajo, tsarin ESP ya taimaka wajen rage radadin tattalin arziki, magance kalubalen kiwon lafiya, samar da ayyuka, da kuma ceton marasa karfi.
Jaridar ta rahoto Akande yana cewa tsarin tattalin arzikin ya kunshi aikin kiwon lafiya, harkar hona, gina gidaje, samar da wuta da abubuwan more rayuwa.
“Mun tsare sana’o’i miliyan daya, mun hana kananan kasuwanci 150, 000 tashi aiki. Mun kuma taimaka wa marasa karfi da tsare-tsaren tattalinmu.”
Tsare-tsarenmu sun taimaka wajen cigaba da tura kudin gaggawa ga talakawan da ke birni.”
Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana yadda suka tsare tattalin arzikin Najeriya. Mataimakin shugaban kasa yace kasuwanci sun tsira duk da annobar COVID-19.