Gwamnatin Tarayya ta Amince Maza da Matansu Suka Haihu da su Tafi Hutun Kwanaki 14

 

Gwamnatin tarayya ta amince da ba maza hutun kwanaki 14 yayin da matansu suka samu karuwa.

Wannan na zuwa ne yayin da ake zaman majalisar zartarwa na mako-mako da ya gudana a Abuja a yau Laraba.

A baya, hukumar NITDA ta samu nasarar ba da irin wannan izini ga ma’aikatar hukumar a watan Maris.

Abuja – Majalisar zartarwa ta tarayya (FEC) ta amince da hakkin hutun kwanaki 14 na haihuwa ga ma’aikatan gwamnatin tarayya maza domin ba su damar sabawa da jariran da aka haifa musu.

Shugaban ma’aikatan tarayya, Dr Folasade Yemi-Esan ce ta bayyana hakan ga manema labarai a fadar gwamnati a ranar Laraba, bayan taron FEC na makon nan wanda Yemi Osinbajo (SAN) ya jagoranta a fadar shugaban kasa da ke Abuja, The Nation ta rawaito.

Ta ce an yi haka ne don ba da damar habaka kauna da kusanci tsakanin uba da jariri, ko haifaffe ko dan riko, musamman a farkon kwanakin rayuwar yaron.

Misis Yemi-Esan ta ci gaba da bayanin cewa ubannin jariran da aka dauka a matsayin ‘yan riko da ba su wuce watanni hudu ba suma za su mori wannan karimcin.

Yadda lamarin ya faro

Wannan ci gaban na zuwa ne watanni bayan gwamnatin tarayya ta amince da hutun haihuwa ga ma’aikatan hukumar bunkasa fasahar sadarwa ta kasa (NITDA).

Da yake jawabi a yayin bikin kaddamarwa da gabatar da yanayin ayyukan ma’aikatan NITDA, wanda aka gudanar a Abuja, ministan sadarwa da tattalin arzikin dijital, ya ce ci gaban ya yi daidai da sabon tsarin aiki na ma’aikata a hukumar.

Kafin amincewa ga ma’aikatan NITDA a cikin Maris 2021, babu wani tanadi na hutun haihuwa ga ma’aikatan gwamnati, yayin da ma’aikata mata ke da damar hutun haihuwa na watanni uku.

Majalisar wakilai, a shekarar 2018, ta yi watsi da kudirin neman ba da hutun haihuwa ga maza masu aure.

A halin yanzu, wasu jahohi a kasar – ciki har da Legas da Enugu – sun amince da hutun haihuwa ga ma’aikata, inji rahoton The Cable.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here