Mun Kammala Duk Wasu Shirye-Shirye da Ake Bukata Wajen Gudanar da Taron APC – Gwamna Ganduje

 

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jahar Kano, ya bayyana cewa a halin yanzun suna jiran a rantsar da shugabannin kananan hukumomi na APC.

Ganduje ya kuma bayyana cewa jaharsa ta kammala shirin gudanar da gangamin taron APC na jaha, wanda ke tafe.

Hakanan kuma ya umarci dukkan muƙarrabansa da su halarci wurin taron bikin murnar ranar samun yancin kai ranar Jumu’a.

Kano – Gwamnan jahar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, yace jaharsa ta shirya wa babban taron APC na jahohi, kamar yadda This Day ta rawaito.

Ganduje yace:

“Mun shirya wa gamgamin taron jam’iyyar APC na jahohi da za’a gudanar ranar 16 ga watan Oktoba, 2021.”

Gwamnan ya faɗi haka ne a wurin taron majalisar zartarwa na gwamnatinsa, jim kaɗan kafin a fara taron, wanda ya gudana a gidan gwamnati, ranar Talata.

“Mun kamala taron gundumomi, haka kuma an gudanar da na ƙananan hukumomi daga baya. Bayan rantsar da shugabannin gundumomi, yanzun muna jiran a rantsar da na kananan hukumomi.”

“Mun shirya zuwan taron APC na jahohi, mun kammala duk wasu shirye-shirye da ake bukata wajen gudanar da shi a jahar mu.”

Kowa ya halarci faretin ranar yanci -Ganduje

Ganduje ya umarci kwamishinonin jahar da mashawarta su halarci taron fareti na musamman ranar samun yancin kai mai zuwa, 1 ga watan Oktoba.

Ganduje ya ƙara da cewa:

“Kwamishinan yaɗa labarai ne zai jagoranci kwamitin shirya bikin murnar zagayowar ranar samun yancin kan Najeriya.”

“Ina umartan dukkan kwamishinoni da masu bada shawara da su halarci wurin ranar Jumu’a, inda za’a yi fareti na musamman.”

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here