Sabon Harin: ‘Yan Sanda Sun Bata, An Kona Mutun da Ransa a Sokoto

 

Kwanaki kadan bayan kai hari sansanin sojoji, ‘yan bindiga sun sake kai hari jahar Sokoto.

Rahotanni sun bayyana cewa, a halin da ake ciki wasu ‘yan sanda sun bata ba a san inda suke ba.

Hakazalika, ‘yan bindigan sun kona wani mutum da ransa yayin da wasu suka jikkata a harin.

Sokoto – Kwanaki biyu bayan kashe jami’an tsaro a sansanin sojoji a Sokoto, ‘yan bindiga sun sake kai wani sabon hari a jihar, Daily Trust ta rawaito.

Sun kai harin ne a karamar hukumar Sabon Birni ta jahar, ranar Laraba 29 ga watan Satumba, inda suka kona wani mutum da ransa kana ‘yan sanda suka tsere.

A Sabon Birnin ne ‘yan bindigar suka kashe akalla jami’an tsaro 17 a farkon makon nan.

Daily Trust ta tattaro cewa an sace mutane 27, ciki har da mata da yara daga Gatawa, wani gari a Sabo Birni.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, dan majalisar mai wakiltar mazabar Sabon Birni ta Gabas a majalisar dokokin jahar, Sa’idu Ibrahim, ya ce a yanzu haka ‘yan bindigan suna kai hare-hare kan hukumomin tsaro a yankin.

A kalamansa:

“Yanzu suna neman inda jami’an tsaro suke domin sun samu karin karfin gwiwa sakamakon harin da suka kai musu a kwanan baya a wani sansanin sojoji a Dama inda aka kashe sojoji da yawa, ‘yan sanda da jami’an Civil Defence.

“Don haka yanzu suna kai hari a wuraren da suka san akwai sojoji, ‘yan sanda ko wani sansanin jami’an tsaro.

“Sun harbe mutane biyu, ciki har da wata mace tare da kona wasu mutane uku da suka buya a cikin kantin hatsi; daya daga cikinsu ya mutu nan take yayin da sauran biyun ke karbar magani a asibiti.”

A cewar dan majalisar, sun mamaye Gatawa ne saboda kasancewar sansanin “Operation Puff Adler” a yankin.

“Yayin da nake magana da ku yanzu, har yanzu ba a ga ‘yan sanda da yawa ba. Ba mu sani ba ko an sace su ko sun gudu.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here