Hukumar NCC ta ƙayyade Mafi ƙarancin Shekarun Mallakar Layin Waya a Najeriya
Hukumar sadarwa ta NCC a Najeriya ta hana yi wa ‘yan ƙasar da shekarunsu bai kai 18 ba rajistan layukan waya.
A wani rahoto da ta wallafa hukumar NCC ta ce sai mutumin da ya kai 18 kawai za a rinka yiwa rajistan layuka.
Read Also:
NCC ta ce wannan mataki nata ya yi daidai da dokokin mallakar layin waya sashi na 70 na kudin bayanan sadarwar Najeriya na 2003.
A lokacin gabatar da wannan tsari gaban masu ruwa da tsaki da kamfanonin sadarwa ciki harda MTN, kamfanin ya bukaci a rage waɗannan shekaru.
MTN ya bukaci NCC ta tsayar da shekara 14 a matsayin mafi kakantar shekarun mallakar layin waya.
Sai dai NCC ta dage akan cewa dole sai mutum ya kai shekara 18 kafin ya mallaki layin waya harda rajista a Najeriya.