Gudanar da Kidaya a Najeriya na Bukatar Kudin da ya Haura Naira Biliyan 187 – NPC
Hukumar Kidiya ta Najeriya ta sanar da cewa biliyan 187 da aka ware a kasafin kudi don kirga al’umma da gidaje, da aka shirya yi a watan Afrilun 2023.
Shugabar hukumar ta riko Ugoeze Mbagou ce ta sanar da hakan ranar Alhamis, a wani taron masu ruwa da tsaki a Abuja.
Read Also:
An sake tada batun sake kidaya a Najeriya a karon farko bayan shekaru 17 da aka yi irinsa a 2006, wanda hakan ya saba shawarar Majalisar Dinkin Duniya da ta shata tazarar shekara 10.
Jaridun cikin gida sun ambaro Mbagou na cewa gudanar da kidaya a babbar kasa kamar Najeriya na bukatar kudin da ya haura naira biliyan 187.
Akan haka ta bukaci a sake duba kasafin kudin don duba yiwuwar kara wani abu.
Sai dai kuma ta ce rabin kudin kidayar zai fito ne daga kungiyoyin da ke bada tallafi ta wannan haujin.