Zargin Cire Sassan Jikin Yaro: Peter Obi ya Jajanta wa Sanata Ekweremadu

 

Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Labour Party a Najeriya, Peter Obi, ya jajanta wa Sanata Ike Ekweramadu kan kama shi da zargin yunkurin cire sassan jikin mutum a Birtaniya.

Obi ya rubuta shafinsa na Twitter cewa ”ni da iyalina muna jajanta wa Ekweramadu kan kaddarar da ta same shi. Muna addu’a, kamar sauran mutane, ga ‘yarsa ta samu sauki, kuma muna fatan Allah zai sa gaskiya ta yi halinta”, in ji Obi.

A jiya ne jami’an tsaro a London suka gurfanar da Ekweramadu da mai dakinsa Beatrice a gaban kotu bisa zargin yunkurin cire sassan jikin mutum.

To amma kotu ta dage zaman har sai farkon watan Yuli mai kamawa.

 

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here