Bayan Kama Shi: An ka sa Samun Layukan Sanata Ike Ekweremadu da Kakakinsa

An lalubi wayoyin salular tsohon mataimakin shugaban majalisa Sanata Ike Ekweremadu da kakakinsa ba a samu ba.

Hakan na zuwa ne a lokacin da mahukunta a kasar Birtaniya suka sanar da kama wani mai suna irin na tsohon kakakin majalisar da matarsa kan zargin safarar sassan jikin bil adama.

Yan sandan na Birnin Landan sun ce an garkame mutanen kuma za a gurfanar da su a gaban kotu a yau Alhamis.

Layukan wayan tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawar Najeriya, Ike Ekweremadu da na Ache Anichukwu, mai magana da yawunsa a halin yanzu suna kashe, Daily Trust ta rahoto.

A ranar Alhamis, yan sanda a Landan sun sanar da kama wasu mata da miji masu suna irin na tsohon kakakin majalisar dattawar na Najeriya Ike Ekweremadu da matar Beatrice Nwanneka Ekweremadu.

Daily Trust ta yi kokarin kiran mutane biyun ta wayar tarho amma layukansu ba su shiga.

A cikin sanarwar, Yan sandan Birnin Landan sun ce:

“An gurfanar da wata mata da miji a yau da laifin hadin baki don shirya tafiyar wani yaro zuwa Birtaniya don cire sassan jikinsa.

“An yi gurfanarwar ne sakamakon bincike da Yan sandan Birnin Landan na sashin laifuka na musamman suka yi.

“Beatrice Nwanneka Ekweremadu, 55 (10.9.66) na Najeriya ana tuhumarta da sufurin wani mutum da niyyar cire wani sashen jikinsa.”

“Ike Ekweremadu, 55 (10.9.66) na Najeriya ana tuhumarsa da sufurin wani mutum da niyyar cire wani sashen jikinsa.”

“An garkamesu kuma zasu gurfana gaban kotun Uxbridge yau.” “An kwace yaron hannunsu kuma ana kula da shi.”

Ekweremadu, wanda ke da gida a Landan, a baya-bayan nan ba a ganinsa a majalisa na yan kwanaki.

A cikin ganin da aka masa a baya-bayan nan a Najeriya, ya ce duk da cewa Labour Party ta tsaya da Igbo a matsayin dan takara, Igbo za su zabi tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar na PDP.

Ekweremadu ya nuna sha’awar gadon Gwamna Ifeanyi Ugwuanyi na Jihar Enugu amma bai samu tikitin takara a PDP ba.

sport guest posting services

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here