Dattawan Arewa Sun yi Kira ga Shugaba Tinubu Kan Korar Ministoci 3

 

FCT, Abuja – Wata kungiyar dattawan Arewa maso yammacin Najeriya ta yi kira ga shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Kungiyar ta ce ya kamata shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi taka tsantsan wajen yunkurin sauya wasu ministoci.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa shugaban kungiyar, Dakta Adamu Giwa ne ya yi kiran ga shugaba Bola Ahmed Tinubu.

An gargadi Tinubu kan korar ministoci 3

1. Ministan gidaje

Wata kungiyar dattawan Arewa maso Yammacin Najeriya ta ce ministan harkokin gidaje, Ahmad Dangiwa ya yi kokari sosai. Kungiyar ta kafa dalilin cewa ministan ya kawo tsare-tsaren da suka kawo sauyi wajen samar da gidaje ga ma’aikata.

2. Ministan kasafin kudi

The Guardian ta wallafa cewa ƙungiyar ta ce ministan tsare-tsare da kasafin kudi, Abubakar Atiku Bagudu ya nuna zalaƙa sosai.

A cewar kungiyar, Atiku Bagudu ya nuna kwarewa wajen fito da tsare-tsaren da suka sanya gwamnati kashe kudi a kan ƙa’ida.

3. Ministan tsaro

Kungiyar ta ce karamin ministan tsaro, Bello Matawalle ya nuna bajinta wajen jawo kashe manyan jiga jigan yan bindiga a Arewa.

Saboda haka shugaban kungiyar ya ce ya kamata shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi sakayya mai kyau ne ga ministocin ba wai korar su ba.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here