Hana Kiwon Fili a Legas: Kungiyar Miyetti Allah ta Bayyana Cewa Farashin Saniya Zai Koma 2m
Kungiyar Miyetti Allah ta makiyaya ta bayyana kokenta kan haramta kiwo a fili a jahar Legas.
Miyetti Allah ta ce, idan aka hana kiwo a fili farashin saniya zai iya kai wa har sama da N2m.
Wannan na zuwa ne yayin da jahar Legas ke kokarin sanya hannu kan kudurin hana kiwo a fili.
Legas – Kungiyar makiyaya ta Miyetti Allah ta bayyana cewa farashin saniya na iya kai wa sama da naira miliyan biyu a jahar Legas idan aka amince da rattaba hannu kan dokar hana kiwo a jahar.
Sakataren shiyyar Miyetti Allah a Kudu maso Yamma ne ya bayyana haka, yayin zaman sauraron ra’ayoyi na kwana daya da majalisar dokokin jahar ta shirya kan dokar hana kiwo a ranar Laraba 8 ga watan Satumba.
Jaridar Punch ta ce majalisar dokokin jahar Legas a ranar Litinin ta aika da kudirin dokar hana kiwo a fili ga kwamitin aikin gona bayan da ta tsallake karatu na biyu.
Read Also:
A yayin taron, Usman ya roki gwamnatin jahar da ta taimakawa makiyaya, lura da cewa kiwon dabbobi ya fi tsada idan aka yi shi a kebe.
Usman, wanda ya amince da cewa akwai wasu makiyaya masu aikata laifuka, ya bayar da hujjar cewa kiwon saniya a wuri guda na iya kara farashin saniya zuwa Naira miliyan biyu.
Ya kuma roki gwamnati da ta bada tallafin kudin kiwon shanu a wuri daya.
A kalamansa:
“Idan ana kiwon shanu a wuri daya, farashin zai iya kaiwa kusan Naira miliyan biyu kowanne. Mun amince da wasu hakimai a wasu jahohi cewa duk wanda ke son kiwon shanu a wani wuri to ya yi rajista kuma ya fadi lokacin da zai tafi.”
Hakanan, Shugaban Kungiyar Mahauta ta Jahar Legas, Alhaji Alabi Bamidele Kazeem, ya ba da shawarar tallafi ga makiyaya shanu, yana mai cewa “kiwon dabbobi a wuri daya yana da tsada”.
A nashi bangaren, Shugaban kungiyar makiyaya tumaki na jahar Legas, Alhaji Mustapha Ibrahim, ya bayyana kudirin a matsayin “wanda zai hada kan kowa da kowa kuma zai tabbatar da alakar da ke tsakanin masu kiwo da manoma”.