korona: Cutar  ta Sake Kashe Wasu Mutune a Najeriya

 

  Hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa a Najeriya ta ce adadin mutanen da annobar korona ta harba a ƙasar sun kai 62,691 bayan da aka gano ƙarin mutum 170 da suka kamu da ita ranar Jumma’a.

NCDC ta ce kazalika, ƙarin mutum uku sun rasa rayukansu sakamakon cutar, wadda ta ɓulla a watan Fabarairun 2020 a ƙasar.

Jihar Legas ce ker da adadi mafi yawa na mutanen da suka kamu a ranar Jumma’a da mutum 106, sai Abuja mai mutum 25.

Oyo na da mutum 14, Edo da Kaduna na da mutum 7-7 kowaccensu da suka kamu da koronar.

Ogun ta samu mutum 4 da suka kamu, sai Bauchi da Benue masu mutum 2-2.

Jihohin Kano da Osun da kuma Rivers na da mutum ɗai-ɗai da suka kamu a kowacce jiha.

Jumillar mutum 58,430 ne suka warke daga cutar kuma aka salleme su, yayin da 1,144 suka rasu zuwa yanzu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here