Dalilin da Yasa Kotu ta Daure’Yan Uwa Biyu

Kotu da ke zamanta a Kaduna ta yanke wa yaya da kanwa hukuncin shekaru 10 a gidan gyaran hali saboda satar N1.7m.

An yi karar ‘yan uwan biyu ne saboda karkatar da naira miliyan 1.7 da suka karba ta hannun gidauniyarsu a matsayin tallafi ga wani mara lafiya.

Sai dai daga bisani sun ki bawa mara lafiyar kudaden suka kuma karkatar da kudin suka yi amfanin kansu da shi.

Wata babban kotu a Jihar Kaduna, a ranar Talata, ta yankewa wasu mata biyu yaya da ƙanwa (Maryam da Rukaiya) hukuncin gidan yari an shekaru 10 saboda satar naira miliyan 1.7 kamar yadda The Punch ta ruwaito.

An gano cewar ƴan uwan biyun da suka mallaki gidauniyar Jamal Health Foundation sunyi amfani da shafinsu na dandalin sada zumunta don neman tallafin kuɗi na taimakawa mara lafiya a 2019.

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa ƴan uwan sun karkatar da kuɗaɗen da suka samu daga hannun ƴan Najeriya sunyi hidimomin gabansu.

Hukumar Yaƙi da Rashawa ta EFCC, cikin sanarwar da Shugaban Sashin Hulda da Jama’ar ta, Wilson Uwujaren, ya fitar ya ce ɗaya daga cikin wanda suka bada tallafi, Badamasi Shanon ya yi ƙorafi kan matan biyu cewa ba suyi amfani da kuɗin don dalilin da suka karba ba.

Wani sashi na cikin sanarwar ta ce, “Wani Alhaji Badamasi Shanono a ƙorafin da ya shigar a 2019 ya yi zargin cewa Gidauniyar Jamal Health Foundation mallakar ƴan uwan biyu ta hanyar amfani da dandalin sada zumunta ta nemi tallafin kuɗi don yi wa wani Usman Umar magani sakamakon rashin lafiya da ke fama da ita na tsawon shekaru biyu.

“Shanono ya yi ikirarin cewa ya bawa gidauniyar tallafin naira miliyan ɗaya yayinda wata mata ta bada N700,000. Ya ƙara da cewa Jamal Health Foundation ta ƙi bawa mara lafiyar kuɗin sai dai ta yi amfani da kuɗaɗen don wasu buƙatun kanta.”

Mai Shari’a Muhammad Tukur ya yanke wa ƴan uwan biyu hukuncin zaman gidan yari na shekaru 10 da zaɓin tarar naira 100,000 bayan sun amsa laifinsu kan tuhumar cin amana.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here