Da yi Yiwuwar Trump zai Je Kotu

An tambayi mutanen Amurka game da sakamakon zaben shugaban kasa.

98% na Amurka da suka shiga zaben ba su goyon bayan Trump ya hakura.

Donald Trump ya bayyana wannan, kila ya kara kwarin gwiwar zuwa kotu.

Alkaluma sun tabbatar da cewa da-dama na mutanen kasar Amurka basu goyon bayan shugaba Donald Trump ya yarda ya fadi zaben da aka yi.

Wani gidan yada labarai ya gudanar da bincike, wanda sakamakonsa ya nuna akasarin jama’a, kusan mutum 200, 000 suna tare da Donald Trump.

Da aka tambayi jama’a ko sun yarda shugaba Donald Trump ya yi na’am da sakamakon zabe da ke nuna Joe Biden ya yi nasara, da-dama sun ce a’a.

A cikin mutanen da su ka kada kuri’arsu a wannan zabe na jin ra’ayi da aka gudanar, mutane 2, 181 ne kacal su ka nemi Trump ya rungumi kaddara.

Ragowar mutane 192, 774 wanda ke nufin 98% na wadanda su ka bayyana ra’ayinsu, sun zabi shugaban Amurkan ya kalubalanci sakamakon zaben.

“Shin Trump ya sallama cewa Biden ya doke shi? A’a: 190,593 (98.9%); Eh: 2,181 (1.1%) Yawan kuri’u: 192, 774.”

Donald Trump ya rubuta: “Dole muyi nasara domin cigaban kasarmu.”

A zaben da aka gudanar a karshen bana, Trump da jam’iyyarsa mai-ci ta Republican, sun sha kashi a hannun ‘dan takarar adawa, Joe Biden mai shekara 68.

Donald Trump ya fara shirin mika ragamar kasar Amurka ga shugaba mai-jiran-gado Joe Biden, amma har yanzu Trump bai yarda an doke shi a zaben bana ba.

Jim kadan bayan an kammala zabe, shugaban Amurkan, Donald Trump ya ce bai amince da nasarar da ake ganin abokin hammayarsa Joe Biden ya samu ba.

Donald Trump ya ce ba kafafen watsa labarai ne za su sanar da wanda ya lashe zaben ba. A karshe dai haka aka yi, aka tabbatar da nasarar jam’yyar adawa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here