Yadda ‘Da da Uwa Suka Bar Duniya

Wani al’amari mai ban tsoro da al’ajabi ya faru a jihar Filato.

Wata dattijuwar mata ta samu labarin kisan dan ta daya tal.

Take a nan ta fadi, washegari da safe tace ga garin ku.

‘Yan uwa da abokan arzikin Theresa Yohanna Bwai, mai shekaru 52 da danta, Bweifar Isaac, mai shekaru 22, suna cikin matsanancin tashin hankali.

Matar ta fadi ta mutu bayan ta samu labarin mutuwar danta daya tal a jihar Filato, shafin Linda Ikeji ya bayyana hakan.

Kamar yadda bayanai suka kammala, wasu ‘yan ta’adda sun harbi Isaac, mai shekaru 22, wanda mawaki ne, mai daukar hoto kuma dalibi ne a jihar Jos, ranar Talata, 17 ga watan Nuwamba da daddare.

Bayan ta samu labarin mutuwar danta, Bwai ta yanke jiki ta fadi, ta rasa ran ta washegari da safe. Za a yi jana’izar uwar da danta a kauyensu Daffo, karamar hukumar Bokkos da ke jihar Filato.

‘Yan uwa da abokan arzikin mamacin sun yi ta wallafa rasuwar a shafukansu na kafar sada zumuntar zamani ta Facebook.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here