Hukuncin da Kotu ta Yanke wa Jagoran ‘Yan Adawa a Cambodia
An haramtawa jagoran ‘yan adawa a Cambodia Kem Sokha duk wani abu da ya shafi siyasa tare daurin shekaru 27 a gidan kaso kan laifin cin amanar kasa.
Ana kallon Kem Sokhaa matsayin babban mai kalubalantar gwamnatin firaiminista Hun Sen.
Read Also:
An zarge shi da hada kai da gwamnatocin kasashen waje, da jam’iyyarsa ta Cambodia National Rescue Party da aka kawo karshenta a 2017.
Sai dai a Kem Sokha ya musanta zarge-zargen da ake ma sa.
Amurka ta yi gaggawar kin amincewa da hukuncin, wanda ya zo watanni kadan gabannin kasar Cambodia ta gudanar da zabe.