Sauraron ƙararakin Zaɓen Shugaban ƙasa: Kotu ta Tafi Hutun Minti 15

 

Kotun da ke sauraron ƙararakin zaɓen shugaban ƙasa a Najeriya ta sanar da tafiya hutun minti 15 domin ci gaba da yanke hukuncin ƙararrakin da ke gabanta.

Mai shari’a Haruna Tsammani da ke jagorantar sharia’r ne ya sanar da tafiya hutun bayan dogon lokaci da ya ɗauka yana karanta hukunci wasu daga cikin shari’un da ke gaban kotun.

A hukuncin da kotun ta yanke kafin tafiya hutun ta kori ƙorafin jam’iyyar APM da ke neman a soke cancantar Bola Ahmed Tinubu, na jam’iyyar APC a zaɓen watan Fabrairu.

Shi ne hukunci na farko a cikin hukunce-hukunce guda uku da kotun za ta yanke yayin zamanta na yau Laraba.

Jam’iyyar APM ta shigar ƙarar a kan Bola Ahmed Tinubu da Hukumar Zaɓe ta INEC da kuma Kabiru Masari, mutumin da ɗan takarar APC a wancan lokaci ya fara gabatar wa INEC a matsayin wanda ke mara masa baya kafin ya sauya shi da Kashim Shettima.

Kotun za ta yanke hukunci kan manyan jam’iyyun adawa na PDP da LP suka shigar gabanta suna kalubalantar nasarar Tinubun

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com