Juyin Mulki: Tsorona ya Tabbata a Gabon Cewa Masu Kwaikwayo za su Fara Aikata Irin Haka – Shugaba Tinubu

 

 

Shugaban kasa Bola Tinubu ya ce yana ta fargabar cewa sojoji za su fara karbe mulki a Afrika bayan juyin mulkin Nijar, inda ya yi misali da Gabon.

Yayin da yake jawabi ga tawagar sulhu na Sarkin Musulmi a kasar da ke makwabtaka, shugaban kasar ya nanata cewa ba abun yarda bane hambarar da gwamnatin damokradiyya.

A cewar shugaban kasar, kowa zai ji a jikinsa idan Najeriya ta bari abun da ya faru a Nijar ya dawwama.

Abuja- Shugaban kasa Bola Tinubu ya bayyana cewa tsoron da ya dunga ji game da juyin mulkin sojoji a Jamhuriyar Nijar ya tabbata da abun da ya faru a Gabon inda sojoji suka tsige Shugaba Ali Bongo ta hanyar kifar da gwamnatinsa.

Shugaban kasar ya ce ya yi fargabar cewa matakin da sojojin juyin mulki a Jamhuriyar Nijar suka dauka zai kafa mummunan tarihi ga nahiyar bakar fata. Fadar shugaban kasa ta bayyana haka a cikin wata wallafa a manhajar X.

Shugaban kasa Tinubu yana tsoron yaduwar juyin mulkin soji a fadin Afrika Gabon ce kasar Afrika da sojoji suka yi juyin mulki a baya-bayan nan bayan wasu manyan janar na rundunar soji sun sanar da kwace mulki a ranar Laraba, 30 ga watan Agusta.

Nan take masu juyin mulkin suka soke zaben da aka yi a kwanan nan sannan suka kawo karshen gwamnatin Bongo ta shekaru 13.

Ya gaji mulki a 2009 daga mahaifinsa wanda ya shugabanci kasar tsawon shekaru 40.

Sai dai kuma, a ranar Alhamis, 31 ga watan Agusta, Shugaban kasa Tinubu ya bayyana tsoronsa lokacin da ya karbi ba kuncin tawagar Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar III a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Tinubu ya yi alkawarin binciko duk wata hanyar diflomasiya don kafa dimokradiyya a Nijar

A cewar shugaban kasar, za a bincika duk wata kofar diflomasiyya tare da masu juyin mulki a Jamhuriyar Nijar kafin daukar matakin amfani da sojoji a matsayin mafita na karshe.

Tinubu ya dage cewa cire gwamnatin damokradiyya ta karfi ba abu ne da za a yarda da shi ba har abada.

“Dole nayi muku godiya saboda ziyara da dama da kuka kai Jamhuriyar Nijar, Masu martaba, amma ya zama dole ku sake komawa. Tsorona ya tabbata a Gabon cewa masu kwaikwayo za su fara aikata irin haka har sai an dakatar da shi. Mu makwabta ne da Jamhuriyar Nijar, kuma abin da ya hada yan Najeriya da manyan mutanensu ba abu ne da za iya rabawa ba. Babu wanda ke sha’awar yaki. Mun ga irin barnar da aka yi a Ukraine da Sudan. Amma, idan ba mu tufkar hanci ba, gaba dayanmu za mu fuskanci sakamakon tare.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com