Gwamna Seyi Makinde Zai Karɓo Bashin N50bn

 

Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo zai karɓo bashin kuɗi Naira biliyan 50 domin gudanar da harkokin gwamnatinsa.

Wannan ya biyo bayan amincewar da majalisar dokokin jihar ta yi wa buƙatar a zamanta na ranar Talata, 5 ga watan Satumba, 2023.

Ya ce zai yi amfani da kuɗin wajen biyan albashi, tallafi da samar da kuɗaɗen kwangilolin da ake kan yi a Oyo.

Jihar Oyo – Majalisar dokokin jihar Oyo ta amince da buƙatar gwamnan jihar, Seyi Makinde, na runtumo bashin kuɗi kimanin Naira biliyan 50 domin tafiyar da harkokin gwamnati.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa majalisar ta amince wa gwamnan ne biyo bayan wasiƙar da ya aika mata ta neman sahalewar ‘yan majalisun kan ciyo bashin.

Shugaban majalisar dokokin, Honorabul Adebo Ogundoyin, shi ne karanta wasiƙar mai girma gwamna a zaman mambobi na ranar Talata, 5 ga watan Satumba, 2023.

A wasiƙar, Gwamna Makinde ya ce:

“Wannan bukatar ta ciyo bashi wani bangare ne na kokarin gwamnati na samar da kudaden da take kashewa akai-akai wadanda suka hada da biyan albashi, tarurruka, da kuma kuɗin ci gaba da kwangiloli daban-daban.”

“Rancen da zamu karɓo na tsawon watanni 45 ne da kuma ƙarin kashi 25% a kowace shekara.”

“Sai dai wannan sharuɗɗa abu ne da za a iya sake dubawa da nazari dai-dai da yanayin musayar kudaɗe a kasuwa.

Majalisa ta amince da buƙatar Makinde Bayan karanta wannan wasiƙa da muhawara kan buƙatar mai girma gwamnan, majalisar dokokin ta amince da runbumo wa al’ummar jihar Oyo bashin waɗan nan kuɗade, Vanguard ta rahoto.

Gwamna Makinde na jam’iyyar PDP na ɗaya daga cikin gwamnonin da suka samu nasarar koma wa zango na biyu a zaɓen ranar 18 ga watan Maris, 2023.

Kuma yana cikin tawagar gwamnonin G-5 na jam’iyyar PDP karkashin jagorancin ministan Abuja kuma tsohon gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com