Badakalar N109.4bn: Kotu ta Soke Belin Mohammed Usman

 

Kotun babban birnin tarayya Abuja ta soke belin daya daga cikin mutanen da ake zargi da yin kwana da kudaden kasa.

An ba da belin Mohammed Usman saboda tsaikon da ya samu a gaban kotu, lamarin da ya fusata alkali.

Ana zargin tsohon AGF da sace kudin kasa tare da wasu da ke aiki a ofishinsa da kuma wani kamfani.

FCT, Abuja – Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Maitama, a ranar Talata, ta soke belin da ta bayar tun farko ga Mohammed Usman, wanda shi ne wanda ake tuhuma na 3 a tuhume-tuhume 14 da EFCC ta gabatar na karkatar da kudaden kasa.

Ana tuhumar Usman ne tare da tsohon Akanta-Janar na Tarayya, AGF, Ahmed Idris kan wasu kudade da aka nema aka rasa a ofishin akanta janar, Vanguard ta ruwaito.

EFCC na zargin cewa Usman wanda shi ne Darakta a asusun tarayya, da kuma wani Godfrey Olusegun Akindele da hadin gwiwar tsohon AGF, sun karkatar da kudaden kasa da suka kai N109.4bn.

Bayanan EFCC sun ce, jami’an sun amfani da asusun wani kamfani mai suna Gezawa Commodity Market & Exchange Limited wajen barnar, wanda shine wanda ake tuhuma na 3 a cikin badakalar.

Yadda aka soke belin A ci gaba da zaman kotun a ranar Talata, mai shari’a Adeyemi Ajayi, ya soke belin wanda ake kara na 3 bayan kasa isa zauren kotun a kan lokaci, Radio Nigeria ta ruwaito.

Usman bai halarci kotun ba ne a lokacin da Alkalin kotun ya shigo zauren da misalin karfe 9:20 na safe, duk da cewa lauyansa, Ibrahim Ishaku, SAN, ya sanar da kotun cewa ya makale ne a gaban kotu.

Cikin rashin gamsuwa da uzurin, Mai shari’a Ajayi ya soke belin wanda ake tuhumar tare da bayar da umarnin tsare shi a gidan yarin Kuje.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here