Miji ya Shigar da ƙarar Surukansa a Kotu Kan Zargin Sun yi Garkuwa da Matarsa

 

Abu kamar wasan kwaikwayo, wani mutumi ya kai ƙarar Surukansa kan zargin sun yi garkuwa da matarsa woto diyarsu a Suleja, jihar Neja.

Mai shigar da ƙara a Kotu daga hukumar yan sanda ya gaya wa Alƙali cewa mutanen biyu sun je har gidan diyarsu sun tafi da ita.

Wannan na zuwa ne a lokacin mutane suka tsinci gawar mutum biyu mace da namiji a Kango duk a yankin na Suleja.

Niger- An gurfanar da iyayen wata matar aure da ke zaune a Kwankwashe, yankin ƙaramar hukumar Suleja, jihar Neja a gaban Kotun Majistire da ke zamanta a Madalla.

Jaridar Daily Trust ta ruwiato cewa hukumar yan sanda ta gurfanar da iyayen matan a Kotu ne bisa zargin sun sace ɗiyar su daga gidan Aurenta.

Mai shigar da ƙara, ASP John Ateni, ya faɗa wa Kotun cewa mutumin da ake zargi, Godgift Ekwedi, da matarsa, Eshima Ekwedi, sun dira gidan ɗiyar su da ke yankin Rafin Sanyi a Suleja, suka yi awon gaba da ita ba tare da izinin mijinta ba.

Bugu da ƙari a cewar mai shigar da karar, sun kwashe kayayyaki a gidan auren ɗiyar ta su wanda a kiyasi sun kai darajar Miliyan biyu da rabi, daga bisani suka cigaba da amfani da kayan.

Wane mataki Kotu ta ɗauka?

Waɗan da ake zargin sun musanta dukkan tuhume-tuhumen da aka ɗora kansu kuma suka nemi Kotu ta ba da belin su.

Alƙalin Kotun, Mai shari’a Ruth Ibrahim, ta bai wa waɗan da ake ƙara beli bisa sharaɗin kawo wanda zai tsaya musu kuma tilas ya zama mazaunin Madalla.

Bayan sauraron ɓangarorin biyu, Alkalin Kotun ta sanar da ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 5 ga watan Satumba, 2022.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here