‘Yan Ta’adda Sun Sake Sako Mutane 7 Cikin Fasinjojin Jirgin Kasa na Abuja-Kaduna

 

Yan ta’addan da suka kai hari a jirgin kasa na Abuja zuwa Kaduna a ranar 28 ga watan Maris, sun sake sako mutum bakwai da suka hada da yan gida daya da mace.

Sunayen wadanda aka sako din sune Abubakar Idris Garba, matarsa, Maryam Abubakar Bobo, babban dansu, Ibrahim Abubakar Garba, mai shekara 10.

Saura sun hada da Fatima Abubakar Garba, mai shekara 7, Imran Abubakar Garba, mai shekara 5 da karamin cikinsu Zainab Abubakar Garba mai shekara daya da rabi.

Abubakar Garba Idris, ma’aikacin hukumar majalisar tarayya, da ne ga tsohon gwamnan mulkin soja na jihar Kano da Benue.

An kuma saki wata mata mai shekaru 60, wata Hajiya Aisha Hassan, wanda aka ce an sako ta ne saboda rashin lafiya da ta ke fama da shi.

Duk da cewa Tukur Mamu, mawallafin jaridar Desert Herald kuma mashawarci a bangaren kafar watsa labarai ga Sheikh Ahmad Gumi, ya janye daga cikin masu sassanci, ya tabbatar da sakin mutanen bakwai ga manema labarai a Kaduna.

Mamu ya ce an saki mutanen bakwai ne bayan shiga tsakani da mai gidansa, Sheikh Gumi ya yi.

Dakaci karin bayani …

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here