Kotu ta Tsige Dan Majalisar NNPP, ta Bayyana na APC a Matsayin Wanda ya Lashe Zaben

 

An haramtawa dan tsagin Kwankwaso kujerar majalisar wakilai biyo bayan rashin gaskiya da ya aikata gabanin zaben majalisa.

An ruwaito cewa, an ba dan takarar jam’iyyar APC kujerar bisa zuwa na biyu a zaben da aka yi a ranar 25 ga watan Fabrairu.

Ba a jihar Kano ba, an yi irin wannan a jihohi daban-daban na Najeriya a bana, inda aka kwace kujerun wasu ‘yan siyasa.

Jihar Kano – Kotun sauraren kararrakin zabe ta Kano ta soke zaben dan majalisar wakilai mai wakiltar Kura/Madobi/Garun Malam a majalisar wakilai.

Kotun dai ta danganta tsige dan majalisar wakilan na jam’iyyar NNPP ne bisa gaza yin murabus daga aikinsa a jami’ar Bayero ta Kano kwanaki 30 gabanin zaben, Daily Trust ta ruwaito.

Don haka mai shari’a Ngozi Azinge ta umarci hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) da ta ajiye takardar shaidar cin zabe da aka baiwa Datti a baya.

Dan tsagin Ganduje a ba nasara

Hakazalika, kotun ta bayyana Musa Ilyasu Kwankwaso na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben a sahihance.

Kwankwaso ne na biyu mafi kuri’u a zaben da aka gudanar a mazabar Kura/Madobi/Garun Malam na Majalisar Wakilai a ranar 25 ga Fabrairu 2023.

Ba a jiyar Kano kadai ba, an samu yanayi irin wannan a jihohi daban-daban na Najeriya saboda wasu matsaloli da aka gabatar a gaban kotun, Vanguard ta ruwaito.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com