Ma’aikatan Lafiya 400,000 sun yi ƙadan a Najeriya – Ministan Lafiya

 

Ministan Lafiya da walwalar al’umma na Najeriya Farfesa Ali Pate ya ce ma’aikatan lafiya 400,000 sun yi ƙadan a Najeriya, idan aka yi la’akari da buƙatarsu da ake yi a ƙasar.

Pate ya bayyana hakan ne lokacin da yake tattaunawa da manema labarai a Abuja a ranar Asabar, bayan wata tattaunawa da aka kwashe kwana uku ana yi tsakaninsa da sauran hukumomi da ke ƙarƙashin ma’aikatar lafiya.

Ma’aikatar ce ta tsara wannan tattaunawa domin fito da wata sabuwar hanya da za a gyara tsarin lafiya a ƙasar.

A cewar Pate waɗannan ma’aikata 400,000 da ake magana sun haɗa da ma’aikatan lafiya da ma su jinya da unguwar zoma da masu haɗa magunguna da masu aiki a ɗakunan gwaji da sauran ma’aikatan da ke taimakawa a ɓangaren lafiya.

“Ba za su isa ba, ko kuna zaton wannan adadin zai iya kula da lafiyar mutum miliyan 220 da ke Najeriya.

“Adadin likitocin da muke da shi a Najeriya ya yi ƙasa sosai da wanda Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce ya kamata kowacce ƙasa likitocinta sukai.

“Akwai damar samar da ƙarin wasu. Ko kuma mu samar da sama da adadin da muke buƙata domin akwai ƙarancinsu a duniya, a yanzu haka akwai ƙarancin ma’aikatan lafiya miliyan 18 a faɗin duniya.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com